<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>232</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Mai kiwona shi Yesu ne,
 Duk tsoro dai ya kawu.
 Ni ba zan rasa kome ba,
 Ga kulawa mai kyau fa!

[V2]
 2) Abinci dai a yalwace,
 Ga ruwan sha domina.
 Ban rasa kome ba domin
 Yesu ne makiyayi.

[V3]
 3) Har raina ma ya wartsake.
 Yanzu dai Yesu ya sa
 Shawararsa ta bi da ni
 A duk tafiyata ma.

[V4]
 4) Har cikin kwarin mutuwa,
 In dai ya sa in je can,
 Tafiya tare mu ke yi,
 Zai tsare ni sosai kuwa.

[V5]
 5) A idon su maƙiyana
 Abinci ma ya shirya.
 Da mai ya shafe kaina har
 Sai daɗi na ke ta ji.

[V6]
 6) Alheri duk da jinƙansa
 Yesu ya sa su bi ni.
 Don haka daɗi na ke ji
 Kullum a wannan duniya.

[V7]
 7) Mai kiwona shi Yesu ne,
 Ba fashi, ko kaɗari ma,
 Har gidansa madauwarni,
 Mu je mu zauna tare.</lyrics>
<title>Mai Kiwona Shi Yesu Ne LW232</title>
</song>